Thursday, 2 November 2017

Abin ya zo: Ramadan Booth ya isa kasar Ingila: Ali Nuhu ya tarbeshi

Taurarin fina-finan Hausa Ali Nuhu(Sarki) da abokin aikinshi jarumi Ramadan Booth kenan a kasar Ingila, sun dauki wannan hoto a filin jirgin kasar Ingilar inda Ramadan ya sauka Alin ya tarbeshi, Ramadan Booth ya isa kasar Ingilar ne domin halartar taron karrama jaruman finafinan nahiyar Afrika karo na ashirin da hudu da wata jarida dake da ofishi a kasar Ingilar me suna African Voice ke shiryawa duk shekara, shidai Ramadan shine zai amshi kyautar karramawa ta jarumin jaruman Kannywood na wannan shekarar.
Ali Nuhu ya tafi kasar Ingil tun kusan kwanaki uku da suka gabata, kuma sai yanzu ne dalilin zuwanshi kasar ta Ingila ya fito fili watau zai yiwa jaruman na fina-finan Hausa da zasu amshi kyautukan karramawa jagora zuwa gurin wannan taro, koda dai akwai wani dalilin na daban daya kaishi to wannan yana daya daga ciki, Lallai Ali ya amsa sunanshi na Sarki.

Jibi Asabarne idan Allah ya kaimu za'a bayar da wadannan kyautukan karramawar.

Sauran jarumai da zasu amshi wannan kyauta ta karramawa sune:

Nafisa Abdullahi.
Hafsat Idirs.
Halima Atete.
Sani Ahmad Yaro.
Me bayar da umarni Kamal S. Alkali.
Sai kuma me shirya finafinai kuma jarumi Hamisu Lamido Iyantama.

Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka kuma ya kaisu duka lafiya ya dawo dasu lafiya.

No comments:

Post a Comment