Wednesday, 29 November 2017

Aiki da hankali: Wasu dalibai da suka gama makarantar sakandire sun ajiye kayan makarantar nasu dan a baiwa daliban da zasu zo nan gaba da basu dashi

Shi aiki da hankali yana da dadi kuma ko wanene yayi abinda ya dace sai kaga mutane sonshi da kuma yabonshi, wannan hotunan sun nuna yanda daliban wata makarantar sakandire dake kasar Afrika ta kudu, bayan sun kammala makarantar, suka nade riguna da wanduna na bai daya(watau Uniform) dinsu suka saka a leda, suka ajiye, dan in an samu wasu dalaibai nana gaba da zasu zo basu da kayan suyi amfani dasu.

Wannan ba karamin abin birgewa bane, lura da irin yanda, bama daliban sakandare ba, har na jami'a wani lokacin idan akace yau ranar gama karatuce to wasu har kayan jikinsu suke yagawa ko kuma duk a rubuce jikin rigunan da sunan murna, saboda ana ganin sun tashi aiki.
Gaskiya wadannan dalibai sun cancanci yabo, tun daga makarantar sakandire, suna da tunabin su taimakawa wanda bashi dashi, ba tare daya tambayesu ba?, wannan abin bigewane, muna musu fatan Aljeri.


No comments:

Post a Comment