Thursday, 2 November 2017

"Aikin yiwa kasa hidimane a yiwa duk macen da ta saka kaya masu nuna surar jikinta fyade">>inji wani lauya a kasar Misira/Egypt

This is not the first time Mr al-Wahsh has caused controversy
Wani sanannen lauya me ra'ayin 'yan mazan jiya dan kasar Misra/Egypt me suna Nabih Al-wahsh yayi wata magana a wani gidan talabijin na kasar data dauki hankulan Duniya kuma ta jawo zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta da muhawara, ana kan tattaunawane akan wata doka da ake shirin yi akan matan banza, sai Nabih yace ai duk ma macen da ta saka kaya masu bayyana tsiraicin ta to aikin yiwa kasa hidimane a yi mta fyade.


Ga ainihin abinda ya fada kamar haka:

"Kana jin dadin ganin mace na tafiya akan titi da bayanta kusan a bude?, ni na fada duk macen da tayi irin wannan shigar to cin mutuncinta kishin kasane kuma yi mata fyade yiwa kasa hidima ne".

Bayan yin wannan maganane akaita cece-kuce a cikin kasar ta Misra, yanzu haka har wata kungiyar kare hakkin mata ta yunkuro zata kaoi gidan talabijin din kara kotu kuma tayi kira ga sauran gidajen talabijin na kasar da su daina baiwa mutane irin su Nabih damar yin maganganun cin zarafin mata.

Haka kuma kungiyar tace shima Nabih din zata kaishi kara kuma sunyi watsi da maganar da yayi inda sukace wannan magana tashi ta yiwa kundin tsarin mulki kasar su daya baiwa mata 'yanci karantsaye.

A watan jiyane aka saka birnin kasar na Cairo ya zama birni na daya a Duniya wajan cin zarafin mata kuma ba'a basu damar samun kulawar lafiya, samun ilimi da kuma samun kud.

A shekarar 2008 wani bincike da akayi ya bayyana cewa kashi tamanin cikin dari na matan kasar sun bayyana cewa an taba cin zarafinsu haka kuma kashi hamsin da hudu cikin dari na maza sun bayyana cewa matanne ke jawowa kansu cin zarafin.

Kodai a watan Octoban shekarar data gabata Nabih ya shiga kanun jaridu da labaran kasar na Egypt bayan wata hira da akayi dashi da wani malami me saukin ra'ayi sukayi a wani gidan talabijin ta kare da zazzafar muhawara atsakaninsu da har takai ga jefe-jefen takalmi da kujeru.

Shidai malamin a wancan lokacin ya bayyana cewa bawai lallai bane a bukaci mace saita rufe gashin kanta da dan kwaliba.

Da fadin wannan magana sai Nabih ya cewa malamin amma kai Kafirine.

Shi kuwa malamin yace kai kuma mahaukacine, ya kamata a kaika gidan gidan mahaukata.

Nan fa Nabih ya cire takalmi zai rafkawa malamin, domin bugawa mutum takalmi ko kuma jifarshi dashi ba karamin wulakancibane a al'adar larabawa, shi kuma malamin yana ganin haka sai ya sungumi kujerar zama, haka suka kama kici-kici har suka fasa wani gilashi, sai ma'aikatan gidan talabijin dinne suka rabasu 

No comments:

Post a Comment