Wednesday, 8 November 2017

Ali Nuhu a kasar Turkiyya

Tauraron fina-finan Hausa Ali Nuhu ya sauka a birnin Istanbul na kasar Turkiyya bayan da ya kammala ziyararshi a kasar Ingila inda yayiwa Nafisa Abdullahi da Ramadan Booth jagoranci zuwa gurin karbar kyautar da aka karramasu da ita acan.

Alin dai dama ya bayyana cewa aiki zai kaishi kasar ta Turkiyya.

Muna mishi fatan Allah ya kiyaye hanya.

No comments:

Post a Comment