Saturday, 25 November 2017

Amina J. Muhammad ta gabatar da jawabi a gurin taron gidauniyar Nelson Madela akan daidaiton maza da mata

Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya,'yar Najeriya daga Arewa, Amina J. Muhammad ta gabatar da jawabi yau a gurin taron gidauniyar marigayi tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela da ake gudanarwa duk shekara.

Amina ta gabatar da jawabine akan muhimmancin baiwa 'ya'ya mata ilimi da kuma kula dasu 'yan da ya kamata da kuma yanda za'a samu daidaito tsakanin maza da mata.
Amina ta yi godiya da damar da aka bata tayi jawabi a gurin taron kuma ta nuna matukar jin dadainta.
Muna mata fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment