Wednesday, 22 November 2017

Aminu Abba Umar, Nomissgee zai yi aure kwanannan

Tauraron me gabatar da shirin Hausa Hiphop a tashar talabijin ta Arewa24 kuma sanannen me wakar gambara ta Hausa, Aminu Abba Umar wanda akafi sani da Nomisgee zai angwance kwanannan, a wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda yace" tabbas gwanannan zanyi aure".

Saidai Nomisgee be bayyana wacece Amaryar tashiba ko kuma yaushene za'a daura auren nashiba.
Muna mishi fatan Alheri shi da amaryar tashi kuma Allah yasa ayi lafiya.

No comments:

Post a Comment