Thursday, 2 November 2017

An daga zaman yafewa Rahama Sadau laifinta zuwa ranar AsabarA ranar Asabar din nan ce shugabannin hadaddiyar kungiyar masu shirya finafinan Hausa, wato Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), za ta zauna domin cire wa Rahama Sadau takunkumin hana ta fitowa a finafinan Kannywood.Idan an tuna, mujallar Fim ta bada labarin cewa a ranar Laraba ta wannan makon ce kungiyar za ta cire wa fitacciyar jarumar takunkumin, bisa wani tabbaci da wata majiya cikin kungiyar ta bai wa mujallar.


Wakilin mu ya tuntubi wasu daga cikin shugabannin kungiyar kan me ake ciki a kan batun yafe wa jarumar tunda ga shi Larabar ta wuce ba a ji komai ba.


Sai su ka ce ba shakka abin da aka tsara kenan tun da fari, to amma zaman bai yiwu ba ne saboda ciwon ido da ya addabi shugaban kungiyar na Jihar Kano, Alh. Kabiru Maikaba (ba ciwon kunne ba kamar yadda mu ka fara ruwaitowa).

Majiyar ta ce yanzu dai kungiyar za ta zauna ranar Asabar din nan domin yanke hukunci kan korar da ta yi wa Rahama Sadau a watan Oktoba na bara.


Majiyar ta kara da cewa yawancin shugabannin kungiyar su na nan kan bakan su na yafe wa jarumar, duk da yake a cikin su akwai wasu tsiraru da su ke ganin bai kamata a yafe mata ba.


Ita dai Rahama Sadau, an kore ta daga Kannywood ne saboda wata rawa da rungume-rungume da ta yi tare da wani mawakin hip-hop mai suna ClassiQ.


MOPPAN ta ce rawar, wadda aka gani a wani guntun bidiyo da ya bulla a karshen watan Satumba na 2016, ta sab'a wa addinin Musulunci da kuma al'adun Malam Bahaushe.


A ganin kungiyar, bullar bidiyon na ClassiQ da Rahama zai k'ara iza mutane su tsani 'yan fim din Hausa, don haka ne aka hukunta ta saboda a nuna cewa shugabannin Kannywood ba su amince da 'yan fim su aikata duk wani mummunan abu a idon jama'a ba.


A makon jiya, Rahama Sadau ta rubuta takardar ban-hakuri ga MOPPAN, inda ta ce in-sha Allahu ba za ta kara aikata abin da ta yi da ClassiQ ba.


Haka kuma ta ziyarci Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, kuma ta yi hira da gidan rediyon Rahama da gidan rediyon Express na Kano inda ta bada hakuri ga al'ummar Jihar Kano.


Fitaccen jarumi Ali Nuhu ne ya shige mata gaba zuwa wannan bada hakuri din.


A hirar sa da mujallar Fim, Ali ya yi nuni da cewa yafe wa Rahama Sadau shi ne abu mafi dacewa, tunda dai hannun ka ba ya rubewa ka yanke ka yar.
Fim Magazine.

No comments:

Post a Comment