Sunday, 12 November 2017

An haifawa Cristiano Ronaldo diya mace: Yanzu 'ya 'yanshi hudu kenan

Tauraron dan kwallon kafa me bugawa kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya samu karuwar Diya mace a yau Lahadi, Ronaldon ya bayyana hakane a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda har tuni ya sakawa diyar tashi suna da 'Alana Martina'.


Ronaldon dai ya taba bayyana cewa burinshi shine ya haifi 'ya'yaye bakwai a rayuwarshi, kuma ga dukan alamu ya dauki hanyar cimma burin nashi domin wannan diya da aka haifa mishi itace ta hudu a cikin jerin 'ya'yan da yake dasu, Critianon yana da 'da me suna Cristianinho da kuma wasu 'yan biyu masu suna Eva da Mateo, sai kuma ga wannan.No comments:

Post a Comment