Wednesday, 8 November 2017

An kori 'yar kasar Amurka daga aiki data zagi jerin motocin shugaban kasa

Wannan wata matace da jerin motocin shugaban kasar Anurka suka zo wucewa ta kusa da ita, tana kan keke, sai ta daga hannu da zagesu, ai kuwa ashe tayi a idon wasu kwararrun maau daukar hoto, inda nan da nan suka dauki hotonta dai-dai lokacin da take zagin.

Da yake kasar da aka cigabane an gano wacece wannan mayar kuma har kamfanin da takewa aiki ya sallameta daga aiki inda ya ce wannan abu da tayi ya sabawa ka'idojin aikin kamfanin.

Wannan batu ya dauki hankulan mutanen kasar har dama waau 'yan kasashen waje inda 'yan kasar suke cewa ai ba tana bakin aikine bane ta aikata wannan laifin wasu kuwa cewa sukayi bata kyautaba.

'Yan kasashen waje kuwa irin su Najeriya cewa sukayi lallai wannan tayi sa'a, inda ace anan Najeriyane to da watakila batakai labari ba, kodai a kamata kokuwa jikinta ya gayamata.

No comments:

Post a Comment