Saturday, 4 November 2017

An yiwa Maryam Gidado nadin Sarautar "Inna Wuron" Kannywood

Kungiyar masu shirya fina-finai na Arewa reshen jihar Zamfara sun yiwa tauraruwar fina-finan Hausar Maryam Gidado nadin sarautar " Inna Wuron" masana'antar finafinan Hausa ta Kannywood, an sakawa Maryam Alkyabba sannan aka bata sandar Sarauta haka kuma aka sakamata Malafa.

Haka kuma an yiwa Abdullahi Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Baba karami nadin Sarauta shima a gurin, amma ya zuwa yanzu bamu san kowace sarautace aka nadashiba amma da zarar mun samu bayani zamu sanar daku in Allah ya yarda.

Muna taya Maryam da Baba karami Murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment