Sunday, 12 November 2017

Ango da amaryarshi:Mahaifin amaryar yaki zuwa gurin shagalin dan ya nuna rashin amincewa da kashe kudi fiye da kima wajan shirya biki

Wani malamin addinin musulunci me suna Farfesa Ishaq Akintola yaki zuwa gurin shagalin bikin diyarshi dan ya nuna rashin amincewarshi da kashe kudi fiye da kima da akeyi a wajaen bikin aure.Kamar yanda ya bayyanawa jaridar Punch yace yaki zuwa wajan shagalinne wanda akasaba yin anko da cinye-ciyen abinci tsakanin 'yan uwa da abokan ango da amarya ne bawai dan baya son diyarshi ko mijinta ba, yace yayi hakanne domin ya nuna rashin amincewarshi akan irin makudan kudin da babu gaira babu dalili mutum bashi da kwai yace sai yayi kuru yayi bikin kece raini, wani ma harda bashi zai ciwo bayan biki yazo ya shiga rigima.

Yayi kira ga gwamnati data sanya haraji me tsauri akan duk wani biki da aka yanka Sa fiye da daya, ya yabi diyatshi inda yace tana da tarbiyya kuma irin diyar da ko wane uba zai yi burin samuce.

A karshe yace idan mutum yana da wadata ba laifi bane ya kashe kudi iya son ranshi wajan hidimar bikinshi amma yana kira ga talaka da ya tsaya daidai matsayinshi.

Wani abu daya kara jan hankulan mutane da wannan biki shine irin yanda amaryar tazo gurin wannan shagali nata sanye da Hijabi, wanda ba kasafai aka saba ganin hakan ba, an saba da ganin amare suna saka irin rigunan nam masu bayyana kafada wasu ma har da kirji.
Muna musu fatan Allah ya albarkaci wannan aure nasu.

No comments:

Post a Comment