Saturday, 25 November 2017

Atiku Abubakar na murnar zagayowar ranar Haihuwarshi

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya cika shekaru 71 da haihuwa a yau Asabar, an haifi Atikune a rana irin ta tau 25 ga watan Nuwamba na shekarar 1946.

A jiyane Atikun ya fitar da sanarwar ficewarshi daga jam'iyya me mulki ta APC kuma anyi kishin-kishin din cewa zai koma tsohuwar jam'iyyarshi ta PDP.

Muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu albarka.

No comments:

Post a Comment