Thursday, 2 November 2017

Atiku dauke da wani yaro dan makaranta a lokacin daya hadu dasu a filin jirgi

Tsohon mataimakin shugaban kasa, wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar kenan dauke da wani yaro, ya hadu da wadannan yaran 'yan makarantane lokacin da malamarsu ta kaisu filin jirgin sama yawan bude ido/kara ilimi kuma akayi sa'a shi kuma Atikun dai-dai lokacin ya dawo daga wata tafiya da yayi zuwa kasar waje.

A jiya ne dai akayi taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC wanda har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta amma Atiku na daya daga cikin jigon jam'iyyar da ba'a gansu a gurin taronba.

Atikun yace yaran sun birgeshi amma abinda ya bashi mamaki shine yanda suna ganinshi suka ganeshi, suka fara fadin Atiku! Atiku!, amma yace yaji dadin haduwa da yaran

No comments:

Post a Comment