Friday, 3 November 2017

Atiku ya musanta labarin dake cewa wai bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zabe me zuwa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya musanta labarin da ake yadawa cewa wai ya bayyana aniyarshi ta tsayawa neman takarar shugbancin kasarnan a zaben shekarar 2019, wasu kafafen watsa labarai sun bayyana cewa sun samu lalabarin Atikun yayi magana akan tsayawarshi takarar a 2019 amma ya fito a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter ya karyata wannan lamari.Atikun dai yaci karo da irin wannan labarinne da wata sanniyar kafar watsa labarai ta wallafa inda ya tambayi cewa "wannan labarin karyar yanata watsuwa a kafafen watsa labarai da dama, ina mamakin wanene ya aika musu dashi(Murmusi)"

Duk da ya karyata wannan labarin wasu masoyanshi sunce su sun kagara dama ya fito ya bayyana wannan aniya tashi saboda haka su kam sunji dadin wannan labari duk da dai cewa ba gaskiya bane.

No comments:

Post a Comment