Tuesday, 28 November 2017

Auren Hadiza Gabon yazo, saura kiris

A kwanakin bayane mukaji labarin cewa Hadiza Gabon ta kusa yin Aure, to ga dukkan Alamu Auren nata ya matso kusa sosai, domin kuwa kamar yanda kuke ganin wannan hoton nata sanye da gyale/kaya, irin na Amare, kuma masu yiwa Amaren kwalliyane suka mata wannan shiri.Hadizar dai ta saka wannan hoton nata da kasa a dandalinta na sada zumunta da muhawara, ta kuma rubuta cewa, ku saurari wani(labari) na nan zuwa, jim kadan sai ta saka wancan dayan hoton na sama, wanda take sanye da kayan Amaren.

Saidai har yanzu Hadizar bata bayyana wanene angon nataba, lokaci dai be bar komi ba, indai muna da rai da lafiya kuma muna taya Hadizar murna, Allah ya tabbatar da Alheri.

No comments:

Post a Comment