Thursday, 9 November 2017

:Babu maraya sai rago:Iyayensu sun rasu tun basu kai shekaru 5 a Duniya ba amma yau gashi Allah ya cika musu burin rayiwarsu

Karin maganar nan da masu iya magana ke cewa babu maraya sai rago haka take, wannan labarin wasu 'yan uwan junane da iyayensu suka rasu tun suna 'yan shekaru 4 dayan kuma yana dan shekaru 2 duka iyayensu suka rasu, sun taso a marayu, karamin cikin burinshi shine ya zama akawu.

Kuma ya nace akan hakan duk da cewa bashi da ko kudin da zai sayi jarabawar tantancewar shiga jami'a da ake rubutawa, watau Jamb, haka dai suka rika aiki suna karatu har yau gashi burin shi ya cika ya zama kwararren akawu wanda aka tantanceshi.

Yayan ne ya wallafa labarin su a dandalinshi na sada zumunta da muhawara kuma ya dauki hankulan mutane sosai inda da yawa suka bayyana cewa tabbas babu maraya sai rago.

No comments:

Post a Comment