Friday, 3 November 2017

"Bani da waya">>Rahama Sadau ta gayawa wani bayan ya tambayeta meyasa bata daukar kira

Wani bawan Allah ya yiwa fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau tambaya a dandalinta na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter cewar wai me yasa idan aka kirasu a waya basa dauka?, to watakila bataji dadin tambayar bane sai ta mayar mishi da cewa "Bani da waya"..


Wannan bakar magana da Rahama ta bashi amsa da ita yasa mutane sunyi sharhi akan wannan batu inda wasu sukace illar yiwa sanan nun mutane magana kenan a bainar jama'a bakasan amsar da zasu baka ba,  wasu kuwa cewa sukayi to siyan waya ya kamashi, a yayin da wasu sukace sai ya bata wayarshi.
Wannan batu ya dan ja hankulan mutane.

No comments:

Post a Comment