Saturday, 4 November 2017

Barawo yaje sata ya makale a taga: Bayan awanni hudu a haka, 'yan sanda sun kamashi

'Yan sanda a kasar Ingila yankin West Midland sun kama wani barawo da yaje sata dubunshi ta cika ya makale a kofar taga, kofar tagar 'yar karamace kuma ta nanne yayi kokarin shiga gidan da zaiyi satar amma dayake asirinshi zai tonu sai ya makale, ya kasa gaba ya kasa baya dole tasa da kanshi ya rika ihu yana kiran a kawo mai dauki.Sai da barawon yayi awanni hudu a haka sannan 'yan sanda sukazo suka fito dashi suka tafi dashi caji ofis, 'yan sandan sun bayyanashi da cewa beda takalmi kuma yana sanye da wandon jins.

Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment