Tuesday, 28 November 2017

Bayan da gwamna El-Rufai ya caccaki Atiku, Mutane sun zakulo wannan hoton

A ranar juma'ar data gabatane da aka fara maganar komawar tsohon shugaban kasa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar jam'iyyar Jam'iyyar PDP, bayan da ya fice daga jam'iyya me mulki ta APC, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai yayi ta sukar Atikun inda ya bayyanashi a matsayin wanda dama can baya taimakawa jam'iyyar.

Gwamna El-Rufai ya kuma fadi cewa Atiku kowace jam'iyya zai koma bazai iya kada shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a zaben 2019.

Bayan kalaman sukar da gwamnan yayiwa Atikune sai mutane suka koma baya suka zakulo wannan tsohon hoton dake nuna Gwamna Nasiru El-Rufai ya durkusa kasa yana gaishe da Atikun.

Mutane da yawa, bayan ganin wannan hoton sun rika kiran gwamnan da sunaye irir-iri.

No comments:

Post a Comment