Wednesday, 29 November 2017

Bayan gama wa'azi a kasar Ingila:Shehk Bala Lau da Kabir Gombe sun wuce kasashen Greece da Jamus


Daga birnin Tottenham Hotspur na Ingila inda Sheikh Abdullah Bala lau da Sheikh Kabiru Gombe suka gabatar da lakca mai taken "Aure A Musulunci".

Malaman sun wuce kasar Greece, daga bisani suka wuce birnin Hamburg, ta kasar Germany, inda A yammacin Laraba zasu gabatar da Wa'azozi a birnin.


Duk da yanayin sanyin xa ake kwadawa a Turai, a hakan suke sanya rigar sanyi kuma su shiga wurare masu sanyi su gabatar da Da'awa, Allah ya saka da alheri, ya bada sa'a.
Wannan hotunan yanda shehunan malaman suka gudanar da wa'azi kenan a wani madallacin kasar Jamus.

No comments:

Post a Comment