Saturday, 4 November 2017

Bbchausa tayi hira da Ali Nuhu da Ramadan Booth

A jiya Juma'a ne kafar watsa labarai ta bbchausa tayi hira da jaruman finafinan Hausa, Ali Nuhu(Sarki) da Ramadan Booth wadanda yanzu haka suke can kasar Ingila dan halartar kayataccen taron karrama jaruman fina-finan nahiyar Afrika da wata mujalla me suna African Voice ke shiryawa, a wannan shekarar Ramadan Booth dinne zai amshi kyautar karramawa ta jarumin jarumai na masana'antar Kannywood.


A yau Asabar ne za'a bayar da wannan kyauta In Allah ya yarda, muna taya Ramadan Booth murna da fatan Allah ya kara daukaka

No comments:

Post a Comment