Monday, 13 November 2017

Buhari Ya Marawa El Rufa'i Baya Kan Shirin Korar Malamai 21, 780


Shugaba Muhammad Buhari ya marawa Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i baya kan shirinsa na korar malaman makarantar Firamare har 21, 780 wadanda suka kasa cikin wata jarrabawar gwajin cancanta da aka shirya masu.Da yake jawabi a wurin taron karawa juna sani da aka shiryawa ministoci Shugaba Buhari ya nuna damuwa kan yadda bangaren ilimin ya tabarbare inda ya yi alwashin ganin cewa gwamnatinsa ta farfado da darajar ilimin.

Shugaba Buhari ya bayar da misali da wani mutum wanda ya ki bayyana sunansa wanda ya shaida masa a shekaru goma da suka wuce inda ya ziyarci makarantar Firamaren da ya kammala don ya bayar da tasa gudunmawa amma abin mamaki sai ya kasa rabe tsakanin dalibai da malaman makarantar. A cewar Buhari abin da mutumin nan ya shaida masa shi ne El Rufa'i ke son aiwatarwa saboda akwai razana , malamin ya kasa cin jarrabawar da ya kamata ya koyawa dalibinsa.

Labari daga rariya.

No comments:

Post a Comment