Saturday, 4 November 2017

Camfe-Camfe a kasar Hausa

Camfi abune wanda ba ayaba ba hadisiba amma mutane suna lakabawa kawunansu kuma idan ka yarda dashi sai ka rika jin yana damunka a zuciya, kamardai yanda ake cewa "tsafi gaskiyar maishi". Ba wai a kasar Hausa kawai ake da camfi ba kowace al'umma nada canfi saidai ya banbanta saboda banbancin zamantakewa da kuma yanayin muhalli.

Ga wasu abubuwa da al'ummar Hausawa suka canfa, wasu ka sansu wasu baka sansu ba:

In zakaje gurin mutum kayi tuntube akan hanya to bazaka sami mutuminba.

Idan hannuka na hagu yana kaikai, in baka sosaba to zaka samu kudu, idan kuma na damane yake kaikao to kaine zaka bayar da kudin.

Idan ka fito daga gida ka hadu da makaho to ka koma babu sa'a a tafiyarka ta wannan ranar.

Idan mace tana rawa a dakinta za'a mata kishiya.Idan ana shara aka share kafar saurayi ko budurwa to bazai samu mata da wuriba ko kuma ba zata samu miji da wuriba, duk abokansu sai sunyi aure sun barsu.

Idan yaro yana leka karkashin kafarshi to kannenshi yake lekowa.

Idan yaro yana tsotsar kafarshi zaiyi binbini(watau duk inda mamanshi taje zai bita).

Idan ka tsallaka fitsarin gwauro kurji zai fito maka.

Idan aka yanka rago jariri yana barci zai yi nasari/munshari.

Idan aka yanka fasa kan ragon suna jariri yana ciwon kai.

Idan ka tsallaka dusa kuraje zasu fito maka.

Idan namiji yana cin abinci da mata zasu kwacemai karfi.

Idan kasan wani Camfi da ba'a rubutashi anan ba kayi comment dashi.

No comments:

Post a Comment