Friday, 17 November 2017

Darasi: shugaban kasar Amurka Donald Trump da yayi suna, tun kamin ya zama shugaban kasa wajan tozarta wani sanata saboda yasha ruwa lokacin yana magana a gaban mutane: Shima Allah ya kamashi yasha ruwa yana magana a gaban mutane

Duniyarnan shiyasa idan kaga mutum yayi abu to karka mai dariya ko kuma ba'a kayi tunanin cewa waikai ka wuce haka ta faru dakai saboda bakasan yanda rayuwarka zata kareba, a shekarun baya wani sanatan kasar Amurka da ake kira da suna Marko Rubio lokacin yana wani jawabi a gaban mutane sai irin bakinshi ya fara bushewa dinnan ya dauko ruwa yasha.


Ai kuwa hakan nafaruwa sai Donald Trump a wancan lokacin ya dauka ya saka wannan mutumin a gaba yayi ta mai tsiya kala-kala yana cewa yayi abinda ba'a tsammaninshi da yi ta yaya zai sha ruwa a gaban mutane lokacin yana jawabi, ai wannan rashin sanin aiki ne.

Ya rika cewa Marko bai iya shan ruwaba, ba da bakin gorar/robar ruwa ake shan ruwa ba, a kofi ake zuwabawa.

Har sharri ya rika yimai yana cewa shi bai taba ganin mutum dake shan ruwa irin Marko ba wai bokiti-bokiti na ruwa ake kawomai yana kwankwadewa dadai maganganu ta tozarci.

Da  Allah ya tashi kamashi sai ga shi jiya Laraba lokacin yana yawabi akan yanda ziyararshi ta kasance a yankin Asia,shugaban kasar Amurka Donald Trump sai ya duka gefen abinda yake magana yace "a'a yaya akayi basu aje ruwa a gurinnan ba, to ba komai", jim kadan sai ga wani ya zo da gorar/robar ruwa ya mikawa shugaban kasar ya kuwa bude ya kwankwada da bakin robar, kamar yanda Marko yayi ya rika mai tsiya yana caccakarshi.

Ai kuwa sai Kasa ta dauka cewa Trump da yake tawa Marko tsiyar shan ruwa lokacin yana jawabi a gaban mutane shima yau gashi Allah ya kamashi yasha.

No comments:

Post a Comment