Sunday, 26 November 2017

"Duk wanda baya tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari nima bani tare dashi"

Wani bawan Allah ya bayya cewa duk wanda baya tare da shugaban kasa Muhammadu buhari to shima baya tare dashi. Ya kara da cewa tabbas yasan shugaba Muhamadu Buhari nada nashi matsalolin, bai yiwa mutane abinda suke tsammanin zaiyi cikin dare daya ba amma har yanzu ba'a sameshi da satar dukiyar talakawaba.

Bashi da halin sata(rashawa ko cin hanci), burinshi shine kawo cigaba me dorewa, bawai yaudaraba.


Tun bayan da wannan mutumin ya wallafa wannan magana tashi akan shugaban kasa Muhammadu Buhari hankulan mutane sun karkata zuwa gareshi, yayinda wasu suka yarda da abinda ya fada, wasu kuwa sunki yadda dashi.

No comments:

Post a Comment