Tuesday, 28 November 2017

"Duk wanda ya auri 'yar kasar Kenya to zai samu garabasar shiga kasar babu shamaki"

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa duk wani dan kasar Afrika daya ga 'yar kasar ta Kenya ya aura to za'a bashi shaidar shiga kasar ta Kenya babi shamaki haka kuma duk wasu dokoki masu tsauri dake aiki akan baki to shi ba zasuyi aiki a kanshiba.

Haka kuma shugaban kasar ya bayyana cewa mutum zai samu izinin zama dama yin aiki ko gida a kasar ta Kenya.

Ya bayyana hakane a wajan rantsar dashi karo na biyu akan kujerar shugabancin kasar ta Kenya.

To sai dai musamman 'yan Najeriya basu amshi wannan albishir da hannu biyu ba, wasu dai sun rika cewa danma kasar Kenya, mun yafe.

No comments:

Post a Comment