Saturday, 25 November 2017

General BMB ya hadu da gwamnan Kano, A.U. Ganduje A gurin taro a Lega sun gaisa: Za'a karramasu

Tauraron fina-finan Hausa da turanci, Bello Muhammad Bello wanda ake kira da General BMB kenan a wannan hoton tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje acan birinin Legas inda kafar watsa labarai ta New Telegraph ta shirya wani gagarumin taro a daren yau dan karrama wasu fitattun mutane da sukayi zarra a fanonin su na ayyuka.
Cikin wadanda za'a karrama a daren na Yau akwai me girma gwamnan jihar Kano din Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan jihar Sokoto dana hamshakin attajiri Alio Dangote da dai sauransu. Muna tayasu murna.

No comments:

Post a Comment