Thursday, 2 November 2017

Gwamnan jihar Kano da tawagarshi sun kaiwa sabon sakataren gwamnatin tarayya ziyarar taya murna

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da tawagarshi sun kaiwa sabon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustafa ziyarar taya murna, gwamnan da sakataren gwamnatin jihar Kano da kwamishinoni da shugaban jam'iyyar APC na Jihar da mataimakinshi duka suka dunguma suka je Abuja Ofishin sabon sakataren dan tayashi muna a tau Alhamis.A cikin jawabin da gwamnan yayi a Ofishin sabon sakataren yace shi da tawagarshi sun kawo mai wannan ziyarane domin tayashi murna akan sabon mukamin da ya samu da kuma tabbatar mishi da cewa gwamnatin jihar Kano zata bashi duk wata gudummuwa da yake bukata da hadin kai wajan ciyar da ksarnan gaba domin akwai bukatar hadin kan gwamnatocin tarayya dana jihohi dan kawowa al'umma romon dimokradiyya.

A jawabinshi da yayi Boss Mustafa yace yaji dadin wannan ziyara da gwamnan da mukarravanshi suka kawomai ya kara da cewa sune mutane na farko da suka kawo mai irin wannan ziyara a hukumance kuma gwamnati zatayi tsare-tsare masu kyau domin kawowa al'ummar jihar Kano abubuwan more rayuwa da cigaba, lura da irin gudummuwar da mutanen jihar suka bayar wajan kamfe da kuma jefawa shugaba Buhari kuri'a har ya zama shugaban kasa.

No comments:

Post a Comment