Wednesday, 15 November 2017

Hatsaniyar kasar Zimbabuwe:Sojoji sun tsige Robert Mugabe daga mulki sun nada tsohon mataimakinshi Emmerson Mnangagwa sabon shugaban kasa

Sojojin kasar Zimbabuwe sun sauke Robert Mugabe daga kan mulki sun saka tsohon mataimakinshi daya kora kwanakin baya watau Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar, haka kuma sun bayyana cewa Robert Mugabe da matarshi suna nan tsare cikin koshin lafiya.Babbar jam'iyya me mulki ta kasar watau ZANU-PF ta tabbatar da wannan sabon nadin shugaban kasar ta dandalinta na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter inda ta bayyana cewa ba juyin mulki akayi ba a kasar tasu, duk abinda sojojin sukayi da amincewar manyan 'yan siyasar kasar.

Kuma kasar Zimbabuwe da jam'iyyar ZANU-PF ba ta Robert Mugabe bace ko kuma ta matarshi, amma suna ta yiwa kundin tsarin mulkin karan tsaye, shiyasa suka dauki wannan hukuncin, wanda yayi daidai da abinda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

No comments:

Post a Comment