Tuesday, 21 November 2017

Hoton Atiku Abubakar yana gaishe da sarkin Kano ya dauki hankalin Mutane

Hoton tsohon mataimakin shugaban kasa, Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar kenan a lokacin da yaje fadar me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II yake mika gaisuwa irin wadda ta dace da sarki, a yayinda shi kuma sarkin yake mika mishi hannu dan su gaisa amma yaki yarda ya bashi.

Wannan hoton ya dauki hankulan mutane sosai a dandalin sada zumunta da muhawara inda mutane suka bayyana mabanbanta ra'ayoyi.

No comments:

Post a Comment