Tuesday, 21 November 2017

Hoton Zahardeen Sani da ya jawomai Allah wadai

Tauraron fina-finan Hausa Zaharadeen Sani Owner kenan a wannan hoton nashi daya saka a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, jikinshi babu riga, da alama mutane basuji dadin ganin wannan hoton nashiba, inda wasu suka rika kiranshi da cewa ya cire hoton be dace ba.

Ko a kwanakin bayama Zaharadeen din ya taba saka irin wannan hoto babu riga wanda shima yasha suka akai. Adam A. Zango ma ya taba saka irin wannan hoto babu riga wanda shima wasu da sukayi sharhi akan hoton sukayi Allah wadai dashi.

Yawanci dai matane akafi samunsu da irin wannan saka hotunan nuna tsiraici da basu dace ba.


No comments:

Post a Comment