Friday, 10 November 2017

Kalli kyawawan hotunan Nafisa Abdullahi: Tana kan hanyar dawowa Gida Najeriya daga Ingila

Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, ga dukkan alamu Nafisar dai na kan hanyar dawowa gida Najeriya daga kasar Ingila inda taje amso kyautar karramawa da aka mata tare da abokin aikinta Ramadan Booth.

Bayan da Ali Nuhu ya musu jagoranci zuwa gurin amsar kyautukan da aka basu, jaruman sunje filin wasan kwallon kafa na kungiyar Chelsea watau Stamford Bridge inda suka kalli wasa tsakanin Chelsea da Manchester United kuru-kuru ba a kwalba ba, irin hotunan na suka wallafa a dandalinsu na shafukan sada zumunta da muhawara sun nuna yanda sukaji dadin hakan
Daga nanne kuma da alama kowa ya kama gabanshi, domin ba'a sake ganin jaruman tare ba, ita Nafisa taje ziyara gurin sannanniyar gadar nan ta birnin Landan, sannan kuma ta shiga wani shago inda tayi siyayya.
Ali Nuhu ya zarce kasar Turkiyya daga Ingila inda ya bar Nafisa da Ramadan acan, yanzu haka yana gida Najeriya ya dawo, to yau itama nafisa gata tana kan hanya, muna mata fatan Allah ya sauke ta lafiya.

No comments:

Post a Comment