Thursday, 2 November 2017

Hotunan yara sanye da irin kayan Kwankwasiyya suna karatun kur'ani sun jawo cece-kuce

Wannan wasu hotunan yarane ga dukkan alamu 'yan makarantar isilamiyane dake sanye da jajayen kaya masu ratsin fari, mazan kuma na sanye da huluna masu ratsin ja, alamar Kwankwasiyya, yaran sun taru suna karatun alkur'anine, saidai abinda bai fito fili ba shin sunayin karatunne dan yiwa kwankwaso addu'a ko kuwa kawai dai wannan hoton an daukeshine  suna cikin ajinsu na marantar isilamiya?.

Wadannan hotunan sun jawo zazzafar muhawara a shadin sada zumunta da muhawara na Facebook inda wani bawan Allah ya wallafasu a dandalinshi.

Wasu dai sun bayya rashin dacewar inda suka rika cewa wannan amfani da addinine dan cimma wani burin siyasa.
 Yayin da wasu kuma sukace ai babu wata matsala a yin hakan domin yin karatun kur'ani da tawassuli dashi wajan neman wata bukata wajan Allah ba laifi bane.
Allah yasa mu dace.

No comments:

Post a Comment