Sunday, 5 November 2017

"Idan na dawo zan baka kyautar sai ka kaiwa mamanka">>Nafisa Abdullahi ta gayawa wani da yace ba ita ya kamata a baiwa kyautar da aka bata a Ingila ba

Tauraruwar Fina-finan Hausa da aka karrama jiya a kasar Ingila da kyautar wadda tayi zarra a cikin jarumai mata bataji dadin wata magana da wani ya mata a dandalinta na sada zumunta muhawara na shafin Twitter ba, mutumin yace" Gaskiya ba ita ya kamata a baiwa kyautar ba", ai kuwa Nafisa na ganin haka sai ta mayar mishi da kakausar amsa.

Inda tace " Inna dawo zan baka ka bawa inna", daga nan dai shi wannan bawan Allah bai sake cewa komaiba, da alama Nafisar ta bashi wannan amsarne cikin fushi.

No comments:

Post a Comment