Thursday, 9 November 2017

Illar da ke tattare da tsoho ya auri karamar yarinya

Dr. ta sha mahawara da malamai kan al'amarin
Jagorar mata a rundunar Hukumar Hisbah ta jihar Kano, Najeriya, Dr. Zahra'u Muhammad Umar, ta ce akwai matsala babba dangane da aurar da kananan yara mata ga tsofaffi.
Ta ce duk da cewa batun tsoho ya auri karamar yarinya wani abu ne da tasha faman tattaunawa a kai, har ma kuma ta fafata da malaman addini masu kare irin wannan muradi.


Kusan za a iya cewa auren karamar yarinya ga tsaffi wani batu ne da ba kasafai ake tattauna shi ba sakamakon rashin haramcinsa a addini da al'ada.
To sai dai Dr Zahra'u ta ce duk da cewa addini bai haramta irin wannan aure ba amma zamani da irin illolin da ke tattare da wannan aure ka iya sa a sanya masa ayar tambaya.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment