Wednesday, 1 November 2017

"Ina godewa Allah da kasancewa musulma: musulunci ya kafu a yankin inyamurai">>Inji A'isha Obi, inyamura data karbi musulunci

Wata baiwar Allah inyamura A'isha Obi wadda ta amshi addini munisulunci hannu biyu-biyu tace tana alfahari da kasancewarata musulma kuma ta tabbata cewa addinin musulunci gaskiyane, A'isha tace musulunci ya samu gindin zama a yankin inyamurai kamar yanda kowane addini irin su kiristanci ya samu zama a yankin, saboda haka tayi kira ga sauran 'yan uwanta inyamurai da suka muslunta da kada suji tsoro su fito suyi addininsu kamar kowa kuma duk wanda ya musu wata barazana su lallabashi ya fito fili su hadashi da hukuma.
A'isha tace itama hakan ya taba faruwa da ita wani ya mata barazana kawai dan tana addinin musulunci, kuma ta hadashi da hukuma, tace duk wanda ya shiga hannun hukuma yasha da kyar to bazai sake yiwa wani barazana ba kuma zai zama darasi ga masu son yin hakan a gaba.


Haka kuma A'isha tayi kira ga wadanda suka amshi addinin musuluncin a yankin inyamuran dasu mike su san addinin a ilimance, tace muaulunta tafi sauki amma sanin addinin shine ke daukar lokaci, tayi kira da cewa kada su yadda aiki ya hanasu neman ilimi.

Allah sarki Allah ya karawa A'isha da sauran dukkan musulmi fahimtar addinin musulunci ya kuma karo mana irinta.

No comments:

Post a Comment