Friday, 3 November 2017

"Kada wanda ya kirani da ranka ya dade">>inji Sabon sakataren gwamnatin tarayya

A ranar larabar data gabatane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon sakataren gwamnati, Boss Mustafa bayan da ya kori  Babahir daga aiki, bayan rantsar dashi dinne kuma sakatare me rikon kwarya ya mika takardun aiki, Boss Mustafa ya bukaci kada wanda ya kirashi da ranka ya dade/mafifici/megirma, ya kara da cewa baisan daga inda mutane suka samo wannan kalmaba domin dai kundin tsarin mulkin kasa da muke amfani dashi bai ambacetaba.Ya kara da cewa koda kalmar shuga me cikakken iko da ake gayawa gwamnoni babu ta a tsarin milkin kasarnan, abin da tsarin mulki ya kira gwamna shine gwamnan jiha kaza kawai.

Saboda haka ya roki duk wanda zai kirashi ko kuma zai ambaceshi a wani guri to yace mai sakataren gwamnatin tarayya kawai, domin kamar yanda yace shi baifi kowane mutum sani ko wayau ba ko hikima sai dai abinda Allah ya albarkaceshi dashi.

No comments:

Post a Comment