Thursday, 30 November 2017

Kalli hoton mataimakin shugaban kasa, Osinbajo tare da shugabn Sudan ta kudu Kiir daya dauki hankulan mutane

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kenan a wannan hoton tare da shugaban kasar Sudan ta kudu watau Salva Kiir, sun hadune a kasar Kenya inda aka rantsar da shugaba Uhuru Kenyatta karo na biyu.

Irin kallon da sukewa juna yasa hoton ya dauki hankulan mutane wasu na tambayar anya wadannan kuwa sunji dadin haduwa da juna kuwa?.

Koda yake dama shi Salva Kiir ba me yawan fara'a bane, kusan koda yaushe fuskarshi a murtuke take.

No comments:

Post a Comment