Tuesday, 21 November 2017

Kalli hotuna daga gidan marigayi Bilya inda matarshi maryam ta hallakashi

A nan hotunan gidan Ma'aurata, marigayi Bilya da matarshi Maryam tayi ajalinshi kenan sanadin wani sakon wayar hannu da akace ta gani a cikin wayarshi wanda shine sanadin da yasa ta aikata abinda ta aikata, hotunan sun nuna baraguzan kwalbar shisha wadda Maryam daga baya rahotanni suka bayyana cewa tayi ikirarin cewa itace mijin nata ya taka ya fadi kasa yaji raunukan dake jinkinshi wanda yayi sanadiyyar mutuwarshi.
Wai dan girman ALlah me yakai shisha gidan ma'aurata?(duk da suna cewa wai ba kwayabace) ta mijince ko ta matarce ko kuwa tare suke sha? hmmmmmm.

Allah ka shiryemu, Ka gafartawa Bilya ka kai rahama kabarinshi da dukkan sauran musulmai da suka rigamu gidan gaskiya.


No comments:

Post a Comment