Wednesday, 8 November 2017

Kalli irin abincin da masu tsaron lafiyar shugaba Buhari ke ci

 Shafinnan na kwarmato labarai me suna Sahara Reporters ya wallafa wadannan hotunan abincin wanda yace irin abincin da masu tsaron lafiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari keci kenan, shafin ya kara da cewa wannan abincin kwata-kwata bashi da kyau kuma be dace ba ganin cewa an ware zunzurutun kudi har naira biliyan daya dan ciyar da masu tsaron lafiyar na shugaban kasa.

Allah sarki Duniya da yawa talakawa na nan basu samu irin wannan abincin ba. Za dai mu saurara muji wane irin martani fadar shugaban kasar zata mayar akan wannan batu.


No comments:

Post a Comment