Saturday, 18 November 2017

Kalli kyawawan hotunan Hadiza Gabon goye da diyarta

Tauraruwar fina-finan Hausa Hadiza Gabon kenan goye da yarinyar da take riko me suna Maryam, bayan harkar Fim, Hadiza Gabon tayi suna wajan tallafawa marasa galihu da kuma marayu musamman yara.


Duk wanda yasan Hadiza Gabon sosai ya santa tare da wannan yarinya Maryam da take riko kuma tana bata kulawa sosai wadda za'a iya cewa koda iyayenta da suka haifeta irin kulawar da zasu bata kenan.
Irin kulawar da Hadiza Gabon ke baiwa Maryam yasa wasu ke tambayar, tana baiwa diyar da ba ita ta haifeta ba irin wannan kulawar, idan ta haifi tata, wace irin kulawa zata bata?.
Muna fatan Allah ya biya Hadiza Gabon ya kuma saka mata da Alheri da wannan kokari da take yi.


No comments:

Post a Comment