Thursday, 9 November 2017

Kalli me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin watsa labarai, Femi Adesina na bacci lokacin da shugaba Buharin ke gabatar da kasafin kudi a majalisar tarayya

Wadannan hotunan na sama sun nuna me baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta fannin watsa labarai Femi Adesina kenan yana bacci shekaran jiya a majalisar tarayya a lokacin da shugaba Buhari yake gabatar da jawabi akan kasafin kudin badi daya gabatarwa majalisar.

Shugaba Buharin dai kamar yanda rahotanni suka bayyana ya shafe sama da awa guda ya na tsaye yana jawabi.

No comments:

Post a Comment