Monday, 27 November 2017

Kalli motar miliyan dari bakwai wadda ke komawa jirgin ruwa in an shiga ruwa da ita


Wannan wata motar alfarmace da kudin ta sunkai naira miliyan sama da naira miliyan dari bakwai, banda kallon da ake mata na matsayin mota kuma za'a iya shiga ruwa da ita a matsayin jirgin ruwa.Motar tana daukar mutane sha biyu, kuma jikinta kadai abin kallone.

Ba kamar kowace mota da ake daga kafa, taku daya kawai a shiga cikintaba, wannan motar tana da matattakala kamar ta bene, yanda mutum zai shigeta cikin kwaciyar hankali.

Ga kuma kujeru na leda masu kyan gani.

Watakila da za'a rufe maka ido a sakaka cikin motar, ba lallaine ka gane cewa kana cikin motaba, zaka iyayin tunanin kana cikin wani dan karamin gidane.

No comments:

Post a Comment