Saturday, 25 November 2017

Kalli Nazir Ahmad saye da tsadajjiyar rigarshi da kudinta suka kai Naira dubu dari uku

 Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin waka  kenan a wadannan hotunan nashi da suka kayatar inda yake sanye da tsadajjiyar rigar kwat dinshi da kudinta suka kai kwatankwacin naira dubu dari uku.


A kwanakin bayane dai Nazir din ya wallafa hoton wannan riga a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya bayyana cewa ya siyeta, yau gashi saye da ita kuma tamai kyau sosai, masoyanahi da yawa sun yaba.
 Nazir dai yayi suna wajan sanya kaya masu tsada da suka hada da takalmi agogo da hawa motocin Alfarma, ko a satin daya gabata saida ya rabawa wasu mutanenshi wayoyi masu dan karen tsada kirar iphone da Samsung. Muna mishi fatan Alheri.


No comments:

Post a Comment