Sunday, 26 November 2017

Kalli yanda akayi kasaitaccen bikin zagayowar ranar haihuwar Halima Atete

A yaune tauraruwar fina-finan Hausa, Halima Atete tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta, Halimar ta shirya kasaitaccen bikin murnar wannan rana me muhimmanci a gareta a otal din Tahir Guest Place dake Kano kuma manya da kananan jarumai da mawaka da masu shiryawa da masu bayar da umarni sunyi tururuwa inda suka tayata murna.


Wasu daga cikin wadanda suka halarci gurin wannan biki na taya Halima murnar zagayowar wannan rana tata sun hada da, Ali Nuhu, Adam A. Zango, Nafisa Abdullahi, Hafasat Idris, Nura M. Inuwa, Saratu Gidado(Daso) dadai sauransu da 'yan uwa da abokan arziki. Akwai gajerun bidiyo akan irin yanda aka gudanar da bikin acan kasa.Godiya ga dukkan masoya, mabiya da makaranta na shafin hutudole.com, godiya ta musamman ga maman Hajara daga jihar Zamfara, sakon ki ya shigo, Allah yabar zumunci.

No comments:

Post a Comment