Thursday, 23 November 2017

Kalli yanda dan sabon shugaban kasar Zimbabuwe ke fariya da kudi

Wannan dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabuwe ne Emmerson Mnangagwa wanda shine za'a rantsar a matsayin wanda zai maye shugaba Robert Mugabe da yayi murabus, Micheal Sean sunan dan nashi kuma a cikin wadannan hotunan an ganshi yana fariya da kudi, wanda hakan yasa wasu ke tambayar anya kuwa?.

Ana tunanin an kori Robert Mugabe wanda yake tattare da zarge-zarge da suka hada dana cin hanci da rashawa, wanda shima a zamaninshi an zargi 'ya'yanshi da matarshi da yin facaka da dukiyar kasar, to ga dan Emmerson shima kamar da alama babu canji.

Lallai 'ya'yan manya suna jin dadinsu.

No comments:

Post a Comment