Sunday, 5 November 2017

Kalli yanda Nafisa ke murnar samun kyautar karramawa a ingila

Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi kenan take nuna murnarta da kyautar karramawa da aka bata jiya a kasar Ingila, ta rubuta a dandalinta na sada zumunta cewa " kyautukan karramawa guda goma sha shida nike dasu kenan zuwa yanzu(kuma wasu na zuwa)."Wannan ba itace kyauta ta farko dana taba samu ba amma tana da matukar muhimmanci a gareni kuma duk wanda ya taimaka min har kawo zuwa haka to ina godiya a gareshi, masoyana inai muku soyayyar da bata misaltuwa, nagode".

Muna taya Nafisa Murna Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment