Saturday, 18 November 2017

Kamfanin yin wayar hannu ta Tecno sunwa Adam A. Zango kyautar sabuwar wayar Phantom 8 me dauke da sunanshi

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, Yarima, Sarkin Nanaye kenan a wannan hoton rike da sabuwar wayar da kamfanin kera wayoyi na Tecno suka aikamishi kyauta, wayar kirar Phantom 8, itace babbar wayar da babu ta sama da ita da kamfanin suka kera, wadda a kasuwa ana sayar da ita akan kudi naira dubu dari da ashirin zuwa dubu dari da arba'in, tazo ne da sunan Adam A. Zango rubuce a jikinta.


Afamun ya nuna wayar cikin farinciki da jin dadi, muna tayashi murna da fatan Allah ya kara dauakaka, arziki.

No comments:

Post a Comment