Wednesday, 1 November 2017

Kanu Nwanko da El-Hadji Diouf sun kaiwa sarkin Kano ziyarar girmamawa: Zasu buga wasa da Kano Pillars

A shirye-shiryen da sukeyi na buga wani wasa na musamman da aka shirya tsakanin tsaffin 'yan kwallo da kungiyar Kano Pillars wanda za'a buga ranar 14 ga watan Disamba idan Allah ya kaimu, Tsohon dan kwallon Najeriya Kanu Nwanko da tsohon dan kwallon kasar Senegal El-Hadji Diouf sun kaiwa sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ziyarar girmamawa.Shidai wannan wasan kwallo an shiryashine dan tara kudin da za'a tallafawa 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa sanna a jawo hankulan mutane dangane da muhimmancin tallafawa 'yan gudun hijirar.
 Kanu da Diouf na cikin wadanda zasu taka leda a ranar In Allah ya kaimu.


No comments:

Post a Comment