Monday, 27 November 2017

Kasar Ehiopia ta gina Kamfanin samar da wutar lantarki me amfani da bola mafi girma a nahiyar Afrika

Gwamnatin kasar Ethiopia ta gina babban kamfanin sarrafa shara mafi girma a nahiyar Afhika da zai rika sarrafa sharar yana bayar da wutar lantarki, Ana sa ran wannan kamfani zai fara aiki a shekarar 2018 idan Allah ya kaimu.

Ana sa ran idan wannan kamfani ya fara aiki zai baiwa kashi talatin cikin dari na gidajen dake babban birnin kasar, Addis Ababa wutar lantarki, kuma za'a rika amfani da kusan kashi tamanin na bolar babban birnin ne a wannan kamfani dan samar da wutar.

Yanda muke da tarin bololi a Najeroya muna bukatar irin wannan kamfani.

No comments:

Post a Comment